Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Ebonyi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Ebonyi, EBSIEC, ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Jossey Eze, ya bayyana hakan a Abakaliki babban birnin jihar, inda ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabanin kananan hukumomi 13 na jihar da Kansiloli 171.
Eze ya ce jam’iyyun siyasa uku a Nijeriya ne suka shiga zaben jihar da suka hada da APC, APGA da LP.
Eze ya sanar da cewa hukumar ta amince da sakamakon zaben kananan hukumomin kamar yadda jami'an hukumar suka sanar da sakamakon zaben kansiloli a wuraren zaben.
Shugaban ya bayyana farin cikinsa da cewa an gudanar da aikin cikin lumana tare da yabawa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki kan irin tallafin da suke bayarwa.
Ya godewa duk masu ruwa da tsaki wajen gudanar da zaben, bisa goyon baya da karfafa musu gwiwa.
Mista Eze ya ce ina mika godiya ta musamman ga gwamnatin jihar kan yadda ba ta yi katsalandan a wajen gudanar da zaben ba, domin hakan ya taimaka wajen tabbatar da zabe mai inganci, da adalci.