Idan shugabanni suka kula da fannin,lafiya,Ilimi da yaki da talauci za a samu gagarumin sauyi a Nijeriya-Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya bukaci shugabanni da su yi amfani da dimbin al’ummar Nijeriya wajen samar da ci gaba a fadin kasar.
Ya bayyana hakan ne a yayin bikin tunawa da ranar yawan jama’a ta duniya, wanda ya ce yana tunatar da dukkan bukatar da ake da ita na magance matsalolin da suka shafi jama’a domin samar da ci gaba a cikin al’umma.
Ya ce idan aka yi la’akari da dimbin matasan da ke da tarin yawa, aka tallafa musu da hanyoyin samun cigaba zai samar da al’umma mai albarka.
Nijeriya a matsayinta na kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka kuma kasa ta 6 a duniya mafi yawan al’umma, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa mai albarka ta fannin albarkar dan Adam, wanda idan aka yi nazari sosai ta hanyar yin abin da ya dace a fannoni 3 mafi muhimmanci na ci gaban al'umma kiwon lafiya, ilimi da yaki da talauci, da kasar za ta samu gagarumin sauyi da ci gaba.