Hukumar NDLEA ta kama wata mata dake kai wa 'yan bindiga alburusai
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya sun cafke wata mata mai suna Ubaida Aliyu mai shekaru 32 dauke da harsashi 573 .
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran hukumar Femi Babafemi, da ya rabawa manema labarai a Abuja.
Sanarwar ta ce ta bisa bincike da akayi matar ta bayyana cewa tana kai alburusan ne ga ‘yan bindiga a jihar Sakkwato.
A cewar sanarwar, an hukumar ta kuma kama wani mutum mai suna Godwin Udochukwu, mai shekaru 35, da laifin shigo da wasu allurai masu illa ga rayuwar al'umma a kan hanyar ta Kaduna zuwa Zariya.
Hakazalika, an kama wani wanda ake zargi mai suna Alkasim Mikailu, mai shekaru 35 a Kano, a wani samame da aka kai masa biyo bayan kama wani ampoules na allurar Diazepam guda 37,880 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hukumar ta yi kira ga sauran al'umma da su cigaba da sanya ido tare da sanar da hukumar bayanai da zarar sunga wani abu da yayi kama da wannan