Kotun ƙoli a Najeriya ta kawo ƙarshen alakar gwamnonin ƙasar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
A wani zama na yanke hukunci ta kotun ta yi Alhamisɗinnan ƙarkashin jãgorancin mai Shari'a Emmanuel Agim ta ce daga yanzu kowace ƙaramar hukuma a ƙananan hukumomin Nigeria 774 ce kadai ke da hurumin sarrafa kuɗaɗen ta.
Kotun ƙolin ta Najeriya ta ce dama dai tsarin mulkin ƙasar matakai uku na gwamnati ya sani wato gwamnatin taraiya, gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi kuma daga yanzu gwamnoni bazasu sake nada kantomomi ƙananan hukumomi ba saboda a cewar kotun gwamnoni suna nada wadan da zasu iya cire su ne kaɗai.
Gwamnonin na Najeriya dai dama sun kulibalanci hurumin kotun na yin Shari'a kan wannan batu, amma a hukuncin da ta yanke kotun ta ce ministan shari'a yana da hurumin shigar da ƙara a gaban ta dan kare kundin tsarin mulkin ƙasar.