Gwamnatin tarayya ta maido da wasu 'yan Nijeriya 190 daga hadaddiyar daular larabawa

Gwamnatin tarayya ta maido da wasu 'yan Nijeriya 190 daga hadaddiyar daular larabawa 


Gwamnatin tarayya ta dawo da jimillan ‘yan Nijeriya 190 daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).


A cewar wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, mai dauke da sa hannun babban daraktan hukumar na shiyyar Arewa ta tsakiya, Bashir Garga, a ranar Talatar nan ta ce, an tarbi wadanda suka dawo a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 5:57 na safe. Tare da tawagar jami'an gwamnati karkashin jagorancin NEMA.


Gwamnatin tarayya ta bukaci dukkan ‘yan kasar, a duk inda suke, da su zama jakadun kasa na gari, tare da kiyaye muhimman dabi’u na kishin kasa,da bin doka da oda, mutunci da mutuntawa.


Idan za a iya tunawa cewa a cikin watan Oktoban shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta dawo da jimillar mutane 542 daga hadaddiyar daular larabawa.


A halin da ake ciki, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ta cimma yarjejeniya da kasar hadaddiyar daular larabawa domin baiwa masu fasfo din Nijeriya damar samun bizar zuwa kasar daga ranar 15 ga watan Yulin 2024.


Ministan yada labaran Nijeriya Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayyar bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp