Gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan $1.5 wajen dakile satar danyen mai - George Akume
Gwamnatin tarayya ta kashe sama da dala biliyan 1.5 daga shekarar 2020 zuwa yau domin kare gidajen man kasar da kuma dakile satar danyen mai.
Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wajen wani taron jin ra’ayin jama’a na majalisar wakilai kan satar danyen mai.
Yace gwamnatin tarayya ta damu da rahoton hukumar kula da masana’antu ta Nijeriya (NEITI) wanda ya nuna sama da dala biliyan 46 da aka sace tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020.
Majalisar dai ta kafa wani kwamiti na musamman karkashin jagorancin shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na majalisar, Alhassan Ado Doguwa, domin ya binciki asarar da aka yi a bangaren mai da iskar gas.
Har ila yau, kakakin majalisar Tajudeen Abbas, wanda mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya wakilta, ya ce an yi asarar dala biliyan 10 a cikin watanni bakwai na satar danyen mai, kuma babu wani sihiri da gwamnati za ta iya yi da irin wannan asara.