Gwamnatin tarayya na kokari wajen magance tsadar farashin kayan masarufi - Ministan Noma
Gwamnatin tarayya ta amince akwai karancin abinci a kasar, sai dai ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana kokarin shawo kan lamarin kuma nan ba da dadewa ba farashin kayayyaki zai sauka.Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce hauhawar farashin kayan abinci ya kai sama da kashi 40 cikin 100 a watannin baya-bayan nan.
Sai dai karamin ministan noma Aliyu Abdullahi ya ce akwai wasu shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke yi na ganin farashin kayan masarufi sun ragu.