Gwamnatin tarayya ba ta sayar da jami'o'i ga 'yan kasuwa ba – Ministan Ilimi
Gwamnatin tarayya ta musanta rahotannin da ke cewa tana sayar da jami’o’in gwamnati ga ‘yan kasuwa.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce an samu wasu na ta yada jita jitar cewa gwamnatin tarayya ta fara sayar da wasu jami'o'i ga 'yan kasuwa.
Ministan wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi da shugabannin hukumomi, ma’aikata da daraktoci a ma’aikatar ilimi a Abuja, ranar Talatar nan, ya ce, Wannan karya ce kwata-kwata kuma babu makamanciyar wannan magana.
Yace shekaru da dama da suka gabata, kamfanoni masu zaman kansu sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da manyan makarantun gaba da sakandare kuma akwai jami’o’i masu zaman kansu a Nijeriya fiye da yadda ake hada jami’o’in gwamnati.
Abin da gwamnati ta yi shi ne bude makarantun gaba da sakandare musamman, jami’o’i don samun gogayya a duniya da ke bai wa wadanda ke aiki a wannan fanni a matakin kasa da kasa damar shigowa kasar tare da kafa cibiyoyi da aka bude domin hadin gwiwa da jami’o’inmu na cikin gida karkashin jagorori.