Gwamnatin Najeriya ta shirya biyan sabon mafi ƙarancin albashi da fansho da ma giratuti inda ta ware Naira tiriliyan uku domin aiwatar da hakan.
Ministan Kasafi da tattalin arziki na ƙasa Atiku Bagudu shiya sanar da hakan a wata ganawa da yayi da kwamitin majalisar dattawa mai sa ido kan yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin ƙasa.
A wannan ganawa da suka yi Juma'ar nan Minista Bagudu ya tabbatar wa 'yan majalisar da 'yan Najeriya cewa ƙarin da shugaba Tinubu ya nemi a sanya a kasafin kudin bana, ba bashi za'a ciyo dan cike gurbin sa ba.