Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a iyakoki kasar kan zanga-zangar da aka shirya

Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a iyakoki kasar kan zanga-zangar da aka shirya

Gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar sakamakon zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki a da tsadar rayuwa a Nijeriya.


A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar shige da fice ta kasa (NIS) KT Udo ya fitar, ya ce kwanturola janar na hukumar ya bayar da wannan umurnin.


Yace shugaban hukumar shige da fice ta kasa, KN Nandap pcc, mms, fsm, ya umurci shugabannin hukumar na Shiyyoyi da Kwanturololi na Jihohi da sauran jami’an na hukumar kula da shige da fice ta kasa da ke fadin kasar nan da su yi taka-tsan-tsan tare da kara sanya ido sossai a ayyukan su. 


Shugaban ya kuma umurci dukkan jami'an kan iyaka da su tabbatar da cewa dukkan su sun yi aiki tukuru don hana wasu 'yan kasashen waje shigowa kasar saboda wata muguwar manufa.


Ya ce yakamata jami'ansu suyi aiki cikin gogewa da kwarewa a yayin wannan aikin domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp