Ƙungiyar masu tãce ɗanyan mai a Najeriya ta koka kan matsayar gwamnatin ƙasar na cigaba da shigo da tãceccen man, abinda suka baiyana da cewa kokarin durƙusar da su ne.
Ƙungiyar tana magana ne bayan wata hira da tace tana yawo da akayi da shugaban hukumar kula da harkokin haƙo tare da tace man fetur na kasar Ahmed Farouk, wanda ya ce dizil da ake tãce a gida Najeriya bashi da kayan wanda ake shigo da shi daga ketare.
Sakataren yada labarai na ƙungiyar ta masu tãce man fetur a Najeriya Eche Idoko ya ce sun damu matuka da kalaman da shugaban hukumar kula da harkokin haƙo da tãce mai Ahmed Farouk yayi na kushe dizil ɗin gida yana yaba na waje, ya ce wannan ba daidai ba ne.
A ranar Juma'an nan ne rahotanni suka ruwaito gwamnatin Najeriya ta bakin wannan hukuma ta NMDPRA ta sanar cewa zata ci gaba da shigo da tãceccen man fetur saboda tabbatar da wadatar sa da kuma kaucewa fadawa hannun bangare guda kachal ke mallakar man da dizil