Gwamnatin Kano ta yi gargadi akan masu yanke bishiyu ba bisa ka'ida ba
Gwamnatin jihar Kano ta yi gargadi ga mazauna jihar kan yadda ake yanke bishiyoyi ba bisa ka'ida ba a jihar, tare da jaddada bukatar dakile illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga muhalli da lafiyar dan adam.
Kwamishinan ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi Nasiru Sule Garo,ne ya bayyana hakan a yayin taro da aka shirya kan tsaftar muhalli a barikin janguza dake Kano.
Muna kira ga jama'a da su goyi bayan kokarin wannan gwamnati ke yi na kara yawan bishiyu domin magance kalubalen sauyin yanayi.
Domin damunar bana tazo da abubuwa da dama don haka sai al'umma sun lura sossai,ta yadda zasu kaucewa gurbatar muhalli da yanayin ka iya kawowa.