Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin aiwatar da mafi karancin albashi


Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon mafi karancin albashi, biyo bayan amincewar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Kaddamarwar ta gudana ne a gidan gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.  

Kafa kwamitin ya zo ne sa'o'i 48 kacal bayan amincewar shugaban kasa. Jihar Kano dai ta zama jiha ta farko a Nijeriya da ta kafa irin wannan kwamiti.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp