Gwamnatin jihar Yobe ta rufe makarantun Firamare da Sakadiren jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta rufe makarantun Firamare da Sakadiren jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare a jihar gabanin zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan ranar 1 ga watan Agustan 2024.


Ma’aikatar ilimi ta jihar ce ta bayyana hakan a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan kula da makarantu, na jihar Bukar M Modu.


Daily Trust ta ruwaito cewa za a rufe makarantu a jihar a ranar Laraba 31 ga watan Yuli, 2024 dama ranar juma’a 2 ga watan Agusta 2024 za a kammala zangon karatu a makarantun  gwamnati da masu zaman kansu.


Takardar ta ce matakin ya zama dole bisa la’akari da shirin gudanar da zanga-zangar a fadin kasar, inda ta kara da cewa makarantun za su koma harkokin su a ranar 15 ga Satumba, 2024.


Da aka tuntubi kwamishinan ma’aikatar ilimi na jihar Farfesa Abba Idriss Adam, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.


Ya ce, ‘’mun san za ai zanga-zanga amma bamu san me zatazo dashi ba,dama anzo karshen zangon karatu wanda za'a gama a ranar juma’a, 2 ga Agusta, 2024, don haka mun yanke shawarar rufe makarantun daga ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024 don kare dalibai


"Ko da yake muna da kyakkyawan fata, za mu sami kwanciyar hankali kuma za mu ji daɗi idan waɗannan zanga-zangar ta faru lokacin da waɗannan ɗaliban suke tare da iyayensu a gida.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp