Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed yace, an yanke wannan shawarar ne domin barazanar tsaro, kare rayukan ma'aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya.
Ya bayyana hakan ne a wajen bude taron manema labarai na shekara biyu kan dabarun bayar da rahoton hidimomin kula da lafiya a matakin farko da aka gudanar a Bauchi ranar Talata.
Category
Labarai