Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin sabbin sarakuna 3 masu daraja ta biyu a jihar.
Hakan na zuwa ne bayan rattaba hannu kan sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita na kafa sabbin masarautu masu daraja ta biyu a jihar ta Kano.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta ce Gwamnan ya amince da nadin Alhaji Muhammd Mahraz Karaye a matsayin sabon Sarkin Karaye mai daraja ta biyu, wanda kafin nadin nasa shi ne Hakimin Rogo.
Sanarwar ta kuma ambato Alhaji Muhammd Isah Umar a matsayin sabon Sarkin Rano, wanda kafin nadin nasa shi ne Hakimin Bunkure. Da kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda shi ne tsohon Sarkin rusasshiyar Masarautar Gaya, da yanzu aka nada shi matsayin Sarkin Gaya mai daraja ta biyu.
Sanarwar Sanusi Bature Dawakin Tofa da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce nadin nasu ya fara aiki nan take.