Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a jihar

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a jihar

A ranar Alhamis ne Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura a Jihar.


Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce kwamitin tsaro na jihar ya yanke shawarar takaita zirga-zirgar babura a Zamfara bayan wani taron gaggawa da aka yi a ranar Laraba.


Sanarwar tace Gwamna Dauda Lawal ya sanya hannu kan dokar takaita zirga-zirgar babura daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe a jihar ta Zamfara.


Wannan wani yunkuri ne na kare rayuka da dukiyoyin al'umma, tare da dakile kalubalen tsaro da fadada hanyoyin da gwamnati za ta dauka na karfafa yaki da ‘yan bindiga da sauran munanan dabi’u a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp