A gaggauta kamo wadanda suka kashe basaraken Chanchanji - Gwamnan Taraba

Gwamnan jihar Taraba Agbu Mefas ya bada umurnin a gaggauta kamo waɗanda suka kashe basaraken garin Chanchanji da ɗan sa.

A sanarwar da kakakin gwamnan Emmanuel Bello ya fitar ta nuna cewa gwamnan ya jajanta wa iyalan basaraken da ilahirin jama'ar ƙaramar hukumar Takum kan wannan aika aika.

Sarkin mai suna Kumbiya Tanimu da ɗan sa Yusuf sun gamu da ajalinsu ne a hanyar Chanchanji zuwa Takum bayan sun halarci wani jana'iza a hanyar komawa gida.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp