Gwamnan Jigawa ya ba ma'aikata bashi don su yi noma a daminar bana
Gwamnatin jihar Jigawa ta raba bashi da kayan noma ga ma’aikata 8,432 domin inganta noma a jihar da kuma bunkasa samar da abinci,kwamitin na shirin tallafa wa aikin gona na jihar Jigawa ne ya aiwatar da shirin wanda shugaban ma'aikata na jihar Muhammad K Dagaceri ya jagoranta.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da rancen ga ma’aikatan da suka amfana da shirin Gwamna Umar Namadi a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli, a babban ofishin kamfanin samar da kayan aikin gona na Jigawa (JASCO Limited) Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa an fito da wannan tsarine domin tallafawa ma'aikata da bunkasa aikin noma a jihar.
Ya ce, an zabo mutane 8,432 da za su ci gajiyar shirin bayar da rancen wanda shine na farko kuma za a cigaba da yi.
A cikin wannan adadin mutanen, an zabo mutum 1,815 da zasu amfana da dubu N500,000 don yin noman shinkafa ,yayin da aka zabo 3,403 da suka amfana da N250,000 domin noman gero.
Haka kuma an zabo mutane 2,068,da suka amfana da dubu 250,000 da zasu yi noman dawa.
Shugaban ma’aikatan jihar Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa,kwamitin ya sanya kudirin zabar ma’aikata 14,000 a matsayin kashi na farko na wadanda za su amfana da shirin kuma wanda shine daya bisa hudu na ma'aikatan dake jihar.