Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci shugabannin gargajiya da su dasa akalla bishiya daya a yankinsu domin dakile kalubalen sauyin yanayi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron wayar da kan jama’a na kwanaki 2 wanda Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACRESAL), karkashin ma'aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar ta shirya.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ya yi kira ga al’ummar jihar da su daina sare itatuwa ba tare da maye gurbinsu da wasu ba.
Category
Labarai