Jan kunne ne mai karfi daga sojojin ga masu yunkurin shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, inda suka ce duk da dokar kasa ta aminta da a yi zanga-zangar lumana, to amma fa, inda 'yancin wani ya kare, a nan na wani ya soma, domin kuwa sojojin sun ce ba za su lamunci a tayar da hatsaniya ba.
Hedikwatar tsaron Nijeriya ta hannun daraktan yada labaranta Maj Gen Edward Buba ce dai ta fitar da wannan gargadi ga masu yunkurin shirya wannan zanga-zangar a wani taron manema labarai a Alhamis din nan a Abuja.
Maj Gen Edward Buba ya ce sojoji ba za su zura idanu su ga ana neman barnata dukiyar kasa ba da sunan zanga-zanga.
Ya ce wannan gargadi ya zama wajibi saboda sojojin sun kwakwulo wani shiri daga wadansu bata-gari da ke shirin yin uwa-ma-karbiya ga zanga-zangar, su mayar da ita wani abu daban su je suna farmakar wuraren kasuwancin mutane
Maj Gen Edward Buba ya ce wadansu na son a yi koyi da zanga-zangar da ke faruwa a kasar Kenya, wadda kowa ya gani a kasa cewa ta kazance kuma ta haifar da tashin hankali, a sabili da haka hedikwatar tsraon Nijeriya ba za ta zura ido ta amince wani abu makamancin abin da ke faruwa a Kenya ya zo Nijeriya ba
Jaridar Daily Trust wacce ta ruwaito babban sojan na fadin hakan ta ce ta wasu 'yan Nijeriya da tsadar rayuwa ta jijjiga sun shirya fantsama kan titi daga ranar daya ga wata mai kamawa na Agusta zuwa 10 ga wata.