Sai Kasuwar Mai'adua jihar Katsina aka sai da buhun masara N98,000 a satin nan, amma satin da ya shuɗe N95,000, nan ma an samu karin N3,000 a sati guda.
To a kasuwar Gombi jihar Adamawa N95,000-98,000 kuɗin buhun yake a makon nan, yayin da a makon jiya aka sai da N90,000 -95000.
To a jihohin Kano da Kaduna N90,000 daidai ake sayar da buhun masara mai cin tiya 40 a makon nan, sai dai farashin makon jiya ya banbanta a kasuwannin da ke Arewacin Najeriya, inda aka sai buhun N87,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano, amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna N90,000 aka sai da buhun a makon jiya ma.
To a bangaren Shinkafar Hausa kuwa, ta fi sauki a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da aka sayar da buhunta N140,000 cif a makon nan, haka nan aka sai da a makon jiya.
A kasuwar Karamar Hukumar Girie jihar Adamawa N160,000 ake sai da buhun a satin nan, haka batun yake a satin da ya gabata.
Sai Kasuwar Mile 12 International Market Legos ake sayar da shinkafar Hausa N155,000 a makon nan, amma a makon jiya N160,000 ne kuɗin buhun yake a kasuwar.
N150,000 cif ake sayar da buhun shinkafa 'yar gida a kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan makon.
Hakazalika an sayi buhun Shinkafar Hausa N150,000 daidai a kasuwar Dawanau jihar Kano a satin nan, farashin dai bai sauya zani ba dana makon jiya.
To wannan makon ma Shinkafar waje ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake saidawa N95,000 a wannan makon, yayin da a makon jiya aka saya N90,000.
Sai dai shinkafar Bature ta fi sauki a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ke kudancin Najeriya da aka saya N78,000, amma a satin da ya kare N80,000 cif aka sai da buhun.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna an sayi buhun Shinkafar waje N88,000 a makon jiya, amma a satin nan N86,000 ake sai da buhun, an samu sauƙin N2000 kenan a sati guda.
To Mai'adua jihar Katsina an sayi buhun N85,000 a makon nan, yayin da a makon jiya aka saya N82,000.
N78,000 aka sai da buhun shinkafar waje a kasuwar Zamani jihar Adamawa a makon nan, haka aka sai da a makon da ya gabata.
Ga masu cin garau-garau ko alala koma kosai, farashin wake fari N250,0000 ne a kasuwar Mile 12 International Market Legos a makon nan, haka yake a satin da ya gabata.
N180,000 ake sai da buhun farin wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna a satin nan, farashin dai bai sauya ba da na makon jiya.
To jihar Adamawa N170,000 daidai ake sayar da Buhunta a satin nan da ke shirin karewa, inda a makon jiya aka saya N165,000.
Ita kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi buhun wake kan kudi N178,0000 a satin nan,sai dai N170,000 cif aka sai da Buhunta a makon daya shude.
To a kasuwar Mai'adua jihar Katsina N180,000 ake sayar da Buhunta a satin nan da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon daya gabata aka saya N175-180,000.
Farashin taliya ma dai ya fi tsada a kasuwar Mile 12 International Market Legos da aka sai da kwalin N18,000 a satin nan, hakan kuwa aka sai da a satin da ya gabata.
A jihohin Adamawa da Kaduna N17,500 ake sayar da kwalin taliya,sai dai a makon jiya N16,000 cif ake sayar da kwalinta a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, yayin da a kasuwar Giwa jihar Kaduna aka saya N15,000 daidai.
To a jihar Katsina kwalin taliyar ya kara N500 a satin nan da aka sai da N16,000, inda a makon jiya kuwa aka saya N15,500.
To sai dai farashin kwalin taliyar ya ki sauki a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da ake saidawa N14,000 a satin nan,yayin da a makon jiya aka saya N16,000 cif,an samu sauƙin N2000 kenan a wannan makon.
DCL Hausa A'isha Usman Gebi.