Fãdar shugaban ƙasa na kitsa yadda za'a kama Peter Obi - Ofishin yãɗa labaran Obi

Ofishin yãda labarai na ɗan takaran shugaban ƙasa a jam'iyar Leba party a zaɓen shekara ta 2022 Peter yana zargin fadar shugaban ƙasa da kulla wa Peter Obi maƙarƙashiya da zummar ɓãta masa suna.

Ofishin na harkokin yada labaran Peter Obi ya musanta kalaman kakakin shugaba Tinubu Bayo Onanuga na alakanta ɗan takaran nasu da zanga-zangar da ake ƙoƙarin aiwatarwa a Najeriya.

Ofishin ya ce Bayo Onanuga ya wallafa a shafin sa na twitter cewa Obi da magoya bayan sa ya kamata a ɗora wa alhakin duk wani mummunan abu da zai auku a zanga-zanga da ake ƙoƙarin yi.

Saidai a sanarwar da ofishin na kula da harkar yaɗa labarai na Peter Obi ya fitar ta bakin Yunusa Tanko Asabat ɗinnan ya baiyana cewa zarge zarge marasa tushe da mai magana da yawun shugaban ya ke yi, ba komai bane illa munaƙisar yadda za'a samu dalilin kama Peter Obi a tauye masa hakki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp