Gwamnatin jihar Kano ta ce bata kai ga cimma matsaya ba kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Kwamishinan yada labarai na jihar Baba Ɗantiye ya fadi cewa gwamnatin Kanon tana kan nazarin yarjejeniyar da gwamnatin taraiyar da Kungiyar kwadago suka cimma kafin ta kai ga yanke hukunci kan batun.
A yanzu dai gwamnatin ta Kano tana biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30 ne kuma ta ce babu wani bashi da ma'aikatan jihar ke bin ta