Biden bai dace da tsayawa takarar shugaban kasa ba- Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yace dama Joe Biden bai cancanci tsayawa takara ba kuma a hakika bai cancanci zama a matsayin shugaban kasa ba.
Trump kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican ya bayyana hakane a jiya Lahadi, bayan da shugaban na Amurka ya bayyana cewa bazai yi takara a zaben kasar dake karatowa ba.
Yace ''za mu sha wahala sosai saboda shugabancinsa, amma za mu gyara barnar da ya yi a cikin kankanin lokaci".