Bai wa kananan hukumomi 'yancin gashin kai shine babbar nasarar da Tinubu ya samu ya zuwa yanzu – Ndume
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume, ya ce tabbatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi shi ne babbar nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya samu tun hawansa mulki a shekarar 2023.
A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma’ar nan, Ndume ya bayyana hukuncin kotun kolin a matsayin babbar nasara da shugaba Tinubu ya samu kawo yanzu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Sanatan ya kuma yi kira ga Tinubu da ya gaggauta fara aiwatar da hukuncin kotun ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa dole ne al’ummar kasa su fara jin dadin shugabanci nagari.
Yace tun lokacin da gwamnonin jihohin Nijeriya suka sanya kananan hukumomi a aljihu ake ta samun cece kuce da kuma koma baya ga al'ummar kasa.
Na yi matukar farin ciki da ci gaban da aka samu, kuma ina fatan wannan zai zama farkon samun 'yancin kananan hukumomi a Nijeriya.