Ba ma goyon bayan duk wata zanga-zanga – Gwamnatin Kogi
Gwamnatin jihar Kogi ta ce ba ta goyon bayan duk wata zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar saboda matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki tattalin arziki da ake fama da shi a Nijeriya.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamnatin jihar na goyon bayan kokarin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke jagoranta na gyara tattalin arzikin kasar.
Fanwo ya ce,Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na aiki tukuru don ganin tattalin arzikin kasar ya ya daidaita.
Yace gwamnatin tarayya ta bullo da wasu hanyoyin karfafa tattalin arziki don magance kalubalen da ake fuskanta na matsin rayuwa da al'umma ke ciki, na habbaka harkokin noma,masana'antu, ilimi da kiwon lafiya a kasa baki daya.
Don haka al'umma su kara hakuri,domin gwamnatin tarayya tana kokari wajen bijiro da sabbin hanyoyin inganta tattalin arziki.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a tsakanin ranakun 1 zuwa 15 ga watan Agusta domin nuna adawa da tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki.