Gamayyar kungiyoyin jam'iyyar APC na Arewa ta tsakiyar Nijeriya na zawarcin Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da ya ajiye jam'iyyarsa ta PDP ya koma jam'iyyar APC.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Saleh Mandung Abdullahi a cikin wata sanarwa da ya aike wa DCL Hausa, ya ce kiran ya zamo wajibi domim burinsu shi ne jam'iyyar APC ta kara bunkasa, amonta ya kai ko'ina.
A cikin wasikar mai taken "gayyatar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam'iyyar APC" ta ce a 'yan kwanakin nan sun gana da masu ruwa da tsaki da jigogin jam'iyyar APC na arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda suka bukaci da a sada gwamnan da takardar gayyata, ta ya koma APC.
Hon Saleh Zazzaga ya ce tuni sun fara isar da sakon ga Gwamnan ta hanyar kafafen sadarwa, yanzu kuma sun mika masa wasika a hukumance.
Kungiyar ta ce kiran nasu ga Gwamnan jihar zai ba APC damar sake karbar jihar Plateau bayan da ta rasa ta a zaben shekarar 2023.
Wasikar ta yi nuni da cewa Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwangne tilo daga yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya da ba dan jam'iyyar APC ba, don haka ne suke bukatarsa da ya saje da sauran 'yan'uwansa.