Anyim zai samu dama daidai da kowa a jam'iyyar APC – Ganduje
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya tabbatar wa tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim,cewa zai samu dama daidai da sauran mutanen dake cikin jam'iyyar.
Ganduje ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi pius a cikin jam’iyyar APC bayan da yabar jam’iyyar adawa ta PDP a ranar Asabar.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban jam’iyyar APC, Edwin Olofu ya fitar a Abuja ranar Lahadi ya fitar.
Ganduje ya bayyana zuwan Anyim da sauran mutanen jam’iyyar APC a matsayin wata babbar ni’ima ga jam’iyyar.
Ya ce, na yi farin ciki da karbar irin wannan muhimmin babban mutum ga jam’iyyarmu, ina so in tabbatar muku a madadin shugaban kasa Bola Ahmed Timubu cewa, muna maka maraba da zuwa babbar jam’iyyar siyasa a Afirka.
Ku tabbata cewa za mu ba ku dama daidai gwargwado kamar tsofaffin ’ya’yan jam’iyyarmu domin ku zo mu hadu muyiwa jam'iyya aiki dan kaiwa ga Nassara.