An yi zanga-zangar rashin tsaro a kauyen jihar Katsina

Dikko Umar Raɗɗa 

Al'ummar garin Marabar Kankara dake kan hanyar Funtua zuwa Malumfashi a jihar Katsina na gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin tsaro.

Jama’ar garin sun rufe hanyoyin wucewar motoci, lamarin da ya kawo tsaiko ga matafiya.

A cewar Al'ummar yankin sunce suna gudanar da zanga-zangar ne sakamakon rashin tsaro da ya addabi yankin.

Ko a ranar Juma'ar data gabata yan bindiga sun hallaka mutane da dama a cikin gona kinsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ya tafi kasar waje domin gudanar da hutun aiki na tsawon wata daya .daya dauka.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp