An bukaci kwamitin binciken Hisba a Katsina ya bada rahoto cikin kwana goma

 


Sakataren gwamnatin jihar Katsina Abdullahi Faskari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Talata a madadin mataimakin gwamnan jihar Faruq Jobe a ofishinsa dake cikin sakatariyar jihar Katsina.

Ya ci gaba da cewa ana sa ran kwamitin zai binciki wasu zarge-zargen cin zarafi da azabtarwa da jami’an hukumar ke yi.

Sauran sharuddan kwamitin a cewar Faskari sun hada da: nazarin dokar kafa hukumar da wasu kura-kurai da ake zargin ta da take hakkin dan Adam.

Kwamitin dai zai kasance karkashin jagorancin kwamishinan matasa da wasanni Aliyu Lawal Zakari yayin da babban sakataren ma'aikatar harkokin addini zai kasance mamba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp