Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu dakunan karatun dalibai a jami'ar tarayya ta Nassarawa
Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu dakunan karatu a tsangayar koyar da fasaha ta Jami’ar Tarayya ta Lafia a jihar Nasarawa, lamarin da ya kawo cikas ga yin karatu ga daliban a sassan da abin ya shafa.
Wasu dalibai da suka bayyana rashin jin dadinsu kan lamarin,sun bayyana cewa ambaliyar ruwan ta dagula karatunsu sosai, wanda hakan ya sa suke shan wuya wajen gudanar da karatu a zauren da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Sun yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihohi da su shawo kan lamarin, musamman ganin yadda jarrabawar su ta gabato.
Sun yi gargadin cewa ba tare da daukar mataki cikin gaggawa ba, za a iya yin illa ga karatun su tare da ruguza gine-ginen jami'ar.