Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 228 a wani yanki na jihar Sokoto

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 228 a wani yanki na jihar Sokoto

Da yawa daga cikin mazauna karamar hukumar Gada da ke jihar Sokoto sun rasa matsuguni, gonakinsu, da gidaje 228 da dabbobinsu sakamakon ruwan sama da aka yi a kwanakinnan nan.


Wasu daga cikin al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da Dantudu, Balakozo, Gidan Tudu, da kuma garin Tsitse.


Sakamakon tantancewar da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) suka gudanar a yankin, da lamarin ya fi shafa shi ne kauyen Dan Tudu, inda gidaje 62 da gidaje 71 suka shafa. A kauyen Balakozo kuma gidaje 33 da gidaje 48 ne lamarin ya shafa.


Hakazalika lamarin ya shafi gidaje 38 da gidaje 52 a kauyen Gidan Tudu, gidaje 68, da kuma 89 a cikin garin Tsitse duk a karamar hukumar ta Gada.


Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Dan Tudu, Balakozo, Gidan Tudu, da garin Tsitse sun kai 1,664.


Hukumomin kuma sun gano cewa dabbobi da dama da suka hada da tumaki da awaki sun bace saboda rugujewar gine-gine a lokacin ruwan sama.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp