A shirye nake na sayar wa NNPCL da matatar fetur da na gina - Dangote

 

Dangote ya ce a shirye yake ya sayar da matatar fetur dinsa ga kamfanin NNPCL na gwamnatin Nijeriya.

Hamshakin attajirin na Afirka ya fadi haka ne a wannan Lahadi, daidai lokacin da ake tsaka da takaddama tsakaninsa da wasu jami'ai da ke sanya ido kan kula da matatun mai na kasar. 

Dangote a wata hira da jaridar Premium Times ya ce 'idan har suna zargi na da zama mai mamaye kasuwanci, na ba su izini su zo su sayi matatar man fetur din da ake cece-kuce a kanta.'

Matatar da aka kwashe shekaru 10 ana ginawa na da karfin fitar da lita 650,000 ta fetur a kowace rana

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp