Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa (JISIEC), ta sanya ranar 5 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Shugaban hukumar Alhaji Awwal Muhammad ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki, a Dutse babban birnin jihar a ranar Juma’a.
Muhammad ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi 27 na jihar.
Yace a baya hukumar ta sanar da dage zaben, daga watan Yunin 2024, zuwa watan Yunin 2025, bayan da aka yi wa dokar zaben jihar kwaskwarima.
Yace duk da haka, suna sane da hukuncin da Kotun Koli ta yanke na baya-bayan nan ta umurci dukkan gwamnatocin jihohi, da su yi zababbun kananan hukumomi a jihohinsu, da gaggawa.
A bisa bin hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, hukumar zaben ta ga ya zama dole ta koma ga hukuncin da ta kotu ta yanke a baya kan zabukan kananan hukumomi, sannan ta bukaci baki daya da a sake gyara dokar zaben jihar, domin ta bi hukuncin kotun koli. , saboda haka ya sanya ranar Asabar 5 ga Oktoba, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zaben a jihar Jigawa.
Don haka ya bukaci hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya da na addini, jam’iyyun siyasa, kungiyoyi, kungiyoyin mata, shugabannin matasa, kafafen yada labarai da kungiyoyin al’umma da su marawa hukumar baya, domin cimma burin da ake so.
Muhammad, wanda ya jaddada kudirin hukumar na gudanar da sahihin zabe, ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar, a kokarinta na gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci a jihar.