Hamshakin attajirin nan na Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote ya ce gidan da yake zaune a duk lokacin da ya ziyarci Abuja, ba nasa bane, haya yake yi.
Aliko Dangote a wata ganawa da manema labarai a Lagos, ya ce irin himmar da yake da ita na ganin masana'antu sun habbaka a Nijeriya ne ya sa baya da burin gina gidaje a wajen kasar.
Dangote ya bayyana cewa ya taba mallaka gida a birnin London amma ya sayar da shi a shekarar 1996.
Ya ce dalilinsa na kin yin gidaje a Amurka ko Ingila shi ne don ya kafa masana'antu kuma ya rage lokacin da zai rika batawa don ziyarar kadarorin da ya adana a kasashen waje.
Nifa gaskiya rayuwa wanan mutumin Yana daga cikin mutanen dasu mutukar burgeni wallh
ReplyDeleteTo Allah ya kiyaye
ReplyDelete